Siyasa

ADC Ta Kalubalanci INEC, Akan taron da zata gudanar

 

Jam’iyyar adawa ta ADC ta kalubalanci matakin da Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) ta ɗauka dangane da tarukan jam’iyyar, inda ta jaddada cewa za ta ci gaba da shirye-shiryenta duk da rashin amincewar hukumar kan shugabancin kwamitin riƙon ƙwarya.

 

Rigimar ta kunno kai ne bayan INEC ta cire sunan David Mark da na Rauf Aregbesola da sauran mambobin kwamitin ayyuka daga jerin shugabannin da ta amince da su, bisa wani hukuncin kotu.

 

Haka kuma, hukumar ta ayyana ranar 1 ga Afrilu 2026 a matsayin ranar ƙarshe ta karɓar duk wani ƙorafi ko gyara daga jam’iyyun siyasa.

 

Sai dai a wani taron manema labarai da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka gudanar, ciki har da Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi da Rabiu Musa Kwankwaso, sun bayyana goyon bayansu ga ci gaba da gudanar da tarukan jam’iyyar.

 

Da yake jawabi a taron, David Mark ya ce babu wata doka da ta tilasta sai INEC ta sanya ido kafin taron jam’iyya ya zama halastacce, yana mai cewa za su ci gaba da tarukansu ko da hukumar ba ta halarta ba.

 

Haka kuma ya tambayi Bola Ahmed Tinubu dalilin da ya sa ake nuna damuwa kan lamarin.

 

A nasa bangaren, kakakin jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya tabbatar da cewa jam’iyyar ta riga ta sanar da INEC tun ranar 27 ga Fabrairu 2026 game da taron, don haka babu abin da zai hana su gudanar da shi kamar yadda suka tsara, yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button