Siyasa
Mataimakin Gwamnan Kano Ya Yi Murabus

An bayyana cewa Mataimakin Gwamnan Jihar Kano ya yi murabus daga mukaminsa, kamar yadda wata sanarwa daga Kwankwasiyya Movement ta tabbatar
A cikin sanarwar da kakakin ƙungiyar, Habibu Sale Mohammed, ya sanya wa hannu, an ce matakin murabus din duk da cewa yana da wahala, an dauke shi ne domin amfanin al’umma baki ɗaya da kuma tabbatar da daidaito a tafiyar da mulkin jihar.
Sanarwar ta ƙara da cewa wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a harkokin mulki a Jihar Kano.
Sai dai ba a bayyana cikakken dalilin da ya kai ga murabus ɗin ba, lamarin da ke ci gaba da janyo cece-kuce a tsakanin al’umma.




