Labarai

Cin Zarafin Yara Ya Karu a Kano Ta Hanyar tilastasu yin Tallan magungunan gargajiya

An fara nuna damuwa a Jihar Kano kan yadda ake amfani da ƙananan yara wajen sayar da magungunan gargajiya a tituna da kasuwanni, lamarin da ke barazana ga ilimi da lafiyarsu.

 

Rahotanni sun nuna cewa yara kanana na yawo da kekunan talla dauke da lasifika suna tallata magunguna kamar “Mainasara” da “Maganin Gidan Baba Garba BK-BK”, a wasu lokuta ma ba tare da kulawar manya ba.

 

Bincike ya nuna cewa akwai manya da ke daukar yaran aiki, suna turasu wurare daban-daban domin talla, sannan a karshen rana su karɓi kuɗin da aka samu, yayin da yaran ke samun Abun da bai taka kara ya karyaba .

 

Masana sun gargadi cewa wannan dabi’a na hana yara zuwa makaranta tare da jefa su cikin hadurra da lalacewar tarbiyya.

 

Haka kuma an nuna damuwa kan ingancin magungunan da ake sayarwa, inda ake zargin ba su da sahalewar NAFDAC.

 

Masu ruwa da tsaki sun bukaci gwamnati da hukumomi su dauki matakin gaggawa, ciki har da ceto yaran tare da mayar da su makaranta, da kuma hukunta masu amfani da su wajen kasuwanci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button