Siyasa

Tinubu ya zo a lokacin da Najeriya ta fi bukatar mutum irin sa – Fasoranti

Dr. Taiwo Fasoranti, tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Ondo , ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki ne a wani muhimmin lokaci da ƙasar ke fuskantar ƙalubale masu yawa.

 

Fasoranti, wanda ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi a Akure, ya ce gwamnatin Tinubu ta fara magance matsaloli kamar tattalin arziki da tsaro, yana mai cewa darajar naira na nuna alamun daidaituwa yayin da ake ci gaba da gyare-gyare.

 

Ya kuma yaba da shirin Renewed Hope Agenda, yana mai cewa ya fara kawo sauye-sauye masu kyau, tare da kira ga ‘yan ƙasa su ci gaba da mara wa gwamnati baya domin ci gaban dimokuraɗiyya.

 

Fasoranti ya nuna cikakken goyon bayansa ga Tinubu, yana mai cewa yana da yakinin kashi 110 bisa ɗari cewa zai yi nasara a zaɓen 2027, tare da ƙara cewa wa’adi na biyu zai ƙara tabbatar da nasarorin da aka samu.

 

Game da burinsa na tsayawa takarar Sanatan Ondo ta Tsakiya, ya ce ya shiga siyasa ne domin yi wa al’umma hidima da samar da ingantacciyar wakilci. Ya kuma jaddada cewa kwarewarsa da alaƙarsa a Abuja za su taimaka wajen kawo ci gaba ga yankin.

 

A ƙarshe, Fasoranti ya ce ya shirya tsaf domin zaɓen, yana mai nuna kwarin gwiwar samun nasara a zaɓen 2027.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button