Sallah: Gwamnan Sokoto Ya Amince da Biyan Albashin watan Maris Kafin Idi

Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto, ya amince da a fara biyan albashin watan Maris ga ma’aikatan gwamnati tun kafin bikin ƙaramar Sallah domin sauƙaƙa musu shirye-shiryen bukukuwan.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan ya fitar ranar Alhamis.
Sanarwar ta bayyana cewa za a fara biyan albashin ne daga ranar Juma’a, 13 ga Maris, 2026, inda biyan zai shafi ma’aikatan gwamnatin jiha, na kananan hukumomi da kuma masu karɓar fansho a faɗin jihar.
Gwamnan, wanda ke ƙasar Saudi Arabia domin gudanar da ibadar Umrah, ya buƙaci ma’aikata su ci gaba da nuna ƙwazo, jajircewa da gaskiya wajen gudanar da ayyukansu.
Ya ce ma’aikatan gwamnati na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar manufofin gwamnatinsa na Nine-Point Smart Innovative Agenda domin inganta ci gaban Sokoto
A cewarsa, gwamnatinsa ta tabbatar da biyan albashi a kan lokaci tare da fara biyan bashin gratuity da aka gada daga gwamnatin da ta gabata.
Haka kuma ya ce gwamnati ta dauki sabbin ma’aikata 3,000 domin ƙara inganta aiki a ma’aikatu da hukumomin gwamnati daban-daban.
Gwamnan ya kuma buƙaci tsofaffin ma’aikata su taimaka wajen koyar da sabbin ma’aikatan aiki, tare da gode wa al’ummar Sokoto bisa goyon baya da addu’o’in da suke bai wa gwamnatinsa.



