Tinubu ya Nada Hamza Mohammed Salau sabon jakadan Nigeria a kasar Iran

Daga cikin waɗanda aka naɗa akwai Abubakar Musa zuwa Chad, Mohammed Idris Haidara zuwa Netherlands, Bako Adamu Umar zuwa Morocco, Olatunji Ahmed Sulu Gambari zuwa Malaysia, Romata Mohammed Omobolanle zuwa Tanzania, da John Shamah zuwa Botswana.
Sauran sun haɗa da Hamza Mohammed Salau zuwa Iran, Ibrahim Danlami zuwa Kenya, Adeola Mopelola Ibrahim zuwa Benin, Adebayo Emmanuel Ayeni zuwa Belgium, Wahab Adekola Akande zuwa Switzerland, Esther Arewa zuwa Namibia, Joseph John Gergadi zuwa Gabon, Luther Ayo-Kalata zuwa Sierra Leone, Danladi Yakubu Nyaku zuwa Sudan da Bello Dogon-Daji Haliru zuwa Thailand.
Haka kuma, United Kingdom ta riga ta amince da sabon Babban Jakadan Najeriya da aka naɗa, Aminu Dalhatu, yayin da France ta amince da naɗin Ayo Oke.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta kuma tura sunayen sauran jakadun zuwa ƙasashen da za su yi aiki domin neman amincewar su kamar yadda dokokin diflomasiyya suka tanada.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci ma’aikatar da ta gaggauta shirya horaswa ga sabbin jakadun kafin su fara aiki a ƙasashen da aka tura su.




