NNPP Ta Kalubalanci Gwamnan Kano da Ya Sauke Wadanda Ta Ce Kwankwaso Ne Ya Nada masa su

Jam’iyyar NNPP ta bukaci Gwamnan Jihar Kano da ya sauke duk masu mukaman da yake zargin tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ne ya nada masa tun farkon gwamnatin sa.
Kakakin jam’iyyar a Kano, Engr. Ibrahim Karaye, ne ya bayyana hakan yayin da yake magana kan rikicin siyasar da ke faruwa a jihar.
Karaye ya ce idan gwamnan ya dauki wannan mataki na sauke su, zai samu damar nada sabbin mutanen da yake ganin sun dace da tafiyar gwamnatin sa, maimakon ci gaba da zargin cewa wasu ne suka nada masa su.
Ya kara da cewa samun nasarar zama gwamna ba abu ne da aka samu cikin sauki ba, domin an yi aiki tukuru kafin a kai ga wannan matsayi.
Haka kuma ya zargi wasu daga cikin masu goyon bayan gwamnati da cewa suna bin gwamnati ne saboda bukatun kansu, ba wai don kishin ci gaban Jihar Kano ba.




