Dambarwar APC a Kano: Magoya Bayan Gawuna Sun Nemi Mafita a NNPP

Wata ƙungiya mai suna “Gawuna ya kwashemu ya sha kwana damu” da ke goyon bayan tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, ta shirya saukar karatun Alƙur’ani mai girma domin neman yardar Allah kan yiwuwar komawarsa jam’iyyar NNPP
An gudanar da taron ne a masallacin da ke ƙofar gidan Nasiru Yusuf Gawuna, inda ya samu halartar ‘yan jam’iyyar APC da na NNPP, har ma da wasu daga jam’iyyar ADC
A yayin taron, an ji yadda magoya bayan Gawuna ke nuna ɓacin ransu, inda suke zargin cewa an maida jagoransu saniyar ware duk da irin gudunmawar da ya bayar ga jam’iyyar APC a Jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.
Kafin wannan mataki, rahotanni sun nuna cewa ƙungiyar ta kai ziyara ga jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, domin roƙonsa ya jawo Gawuna zuwa cikin jam’iyyar, abin da suka bayyana a matsayin wata hanya ta “ceto” Jihar Kano.
Sai dai wasu masu sharhi na kallon wannan yunƙuri a matsayin wata sabuwar baraka da ka iya kunno kai a cikin jam’iyyar APC, musamman a daidai lokacin da siyasar jihar ke ƙara ɗaukar zafi.




