Gwamnatin kasarnan Ta Fara Kwashen ’Yan Kasarta Daga Iran

Gwamnatin Najeriya ta fara kwashe ’yan ƙasarta daga ƙasar Iran waɗanda suka nemi a dawo da su gida, tare da raka su ta kan iyakar ƙasar Armenia domin tabbatar da tsaron lafiyarsu, yayin da rikici ke ci gaba a yankin Gabas ta Tsakiya.
Jami’an ofishin jakadancin suna bakin iyakar Iran da Armenia domin karɓar waɗanda ke son a kwaso su.
Ta ce an fara samun wasu jiragen da suka taso daga Saudi Arabia zuwa Lagos kwanaki biyu da suka gabata, amma an dakatar da su saboda rufe sararin samaniyar ƙasar.
Shugabar NiDCOM ta tabbatar cewa da zarar an bude sararin samaniyar, tawagar gwamnati da ta ƙunshi jami’ai daga ma’aikatu daban-daban za ta ci gaba da aikin kwashe ’yan ƙasar gida.
Matakin na zuwa ne bayan tashe-tashen hankula da suka fara tun ranar 28 ga Fabrairu, lokacin da aka kai harin soji kan Iran da Amurka da Isra’ila suka yi.




