Labarai

Inuwar Jama’ar Unguwa Uku Ta Karrama Fitattun mutane da suke bawa unguwar gudun mawa ta fuskoki da dama

Kungiyar Inuwar Jama’ar Unguwa Uku ta gudanar da wani babban taro na ‘yan unguwa, inda ta karrama wasu fitattun mutane da suka bayar da gudunmawa wajen cigaban unguwar, ta hanyar basu lambobin yabo.

Daga cikin wadanda aka karrama akwai Mubarak Auwal (Unguwa Uku), ma’ikaci’a Hikima Radio, tare da wasu manyan mutane da suka hada da Farfesa Mustapha Abubakar (FUD), Farfesa Sani Ibrahim Salihu (BUK), Farfesa Rayyan Muhammad Garba (MAUN), da kuma Assoc. Prof. Pharmacist Sulaiman Danladi (BUK).

 

Sauran sun hada da Dr. Ibrahim Aliyu Umar (Zanga), Alhaji Ibrahim Abdullah Tanko “Darling” (Matawallen Tarauni), Alaramma Salisu Kimas, Malam Idris Shuaibu (KUFTA), Malam Shehu Kurma Tela, da kuma Injiniya Abdulhamid Umar (Gidan Tsamiya).

 

A yayin taron, mahalarta sun tattauna muhimman matsalolin da ke addabar unguwar, musamman matsalar ruwan famfo, inda suka bayyana cewa duk da cewa ruwan ya wuce ta titin unguwar, har yanzu bai shiga cikin Unguwa Uku ba.

 

Dangane da haka, al’ummar unguwar sun yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya dubi wannan matsala tare da daukar matakan da suka dace domin magance ta.

 

Taron ya kasance wata dama ta karfafa hadin kai da kuma yabawa wadanda ke bada gudunmawa ga cigaban al’umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button