Shugaba Tinubu ya tafi Birtaniya

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya kama hanya tare da mai ɗakinsa zuwa Birtaniya domin amsa gayyatar ziyarar aiki da fadar Birtaniya ta yi masa.
Wani bidiyo da gidan talbijin na NTA da fadar shugaban ƙasar ta wallafa ya nuna shugaba Tinubu da maiɗakinsa da mukurrabansa sun tashi daga filin Nnamdi Azikwe da ke Abuja zuwa birnin London.
Wannan ce ziyara ta farko cikin shekara 37 da wani shugaban Najeriya ke kai wa fadar bisa gayyatar sarki.
Sarki Charles III na Birtaniya da mai ɗakinsa Saurauniya Camilla ne za su tarbi Shugaban na Najeriya a lokacin ziyarar da aka shirya manyan liyafa.
Ziyarar aiki da shugaban ƙasa ke kaiwa fadar Buckingham ta kasance wata muhimmiyar hanyar inganta alaƙar diflomasiyya tsakanin ƙasashe da Birtaniya, inda ake tattauna hanyoyin cin gajiyar juna.
Rabon da shugaban Najeriya ya kai irin wannan ziyara Birtaniya tun a 1989, lokacin da Janar Ibrahim Babangida ya ziyarci mariganya Sarauniya Elizabeth II, inda ya shafe kwanaki huɗu.
Ziyarar na zuwa ne kwana ɗaya bayan da hare-haren Boko Haram suka yi sanadiyyar mutuwar mutum 23 a jihar Borno.



