Labarai

Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Ya Kafa Kwamitin Aiwatar da ‘Yan Sandan Jihohi

*Abuja, Najeriya* Babban Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), Olatunji Disu, ya kafa wani kwamiti na musamman da zai shiryawa tare da tabbatar da fara amfani da tsarin ‘yan sandan jihohi

Wannan mataki ya biyo bayan umarnin Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, na aiwatar da wannan tsari.

An kafa kwamitin ne a ranar 4 ga watan Maris, 2026, a hedkwatar ‘yan sanda da ke Abuja, yayin wani taro na farko da sabon Sufeto Janar din ya shirya tare da manyan jami’an rundunar.

A yayin taron, IGP Disu ya bukaci manyan jami’an da su zama abin koyi ga jami’an da ke karkashinsu, tare da jaddada muhimmancin tattara bayanan sirri da amfani da fasahar zamani wajen gudanar da ayyukan ‘yan sanda.

Bayan taron, Disu ya bayyana cewa kwamitin zai yi nazarin dokokin aikin ‘yan sanda da bukatun da ake da su, sannan kuma zai tsara hanyoyin da za a bi domin kaddamar da ‘yan sandan jihohi a fadin kasar.

Ya kuma fayyace cewa aikin ‘yan sandan jihohi ba zai shafi aikin ‘yan sandan tarayya ba, a maimakon haka, za su yi aiki tare don karfafa zaman lafiya da tsaro a kasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button