Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu Shaida Ce ga Mutuncin Bello Matawalle

A cikin wata sanarwa da Alhaji Fahad Ogan Boye ya fitar a ranar 26 ga Afrilu, 2026, ya ce waɗannan zarge-zarge na cike da ruɗani da yaudara, tare da zargin cewa wasu na ƙoƙarin ɓata masa suna ne saboda hassada da ƙiyayya.
Sanarwar ta jaddada cewa duk wanda aka samu yana yaɗa irin waɗannan ƙarye-ƙarye zai fuskanci matakin shari’a. Haka kuma, ta tunatar da cewa a baya an taɓa danganta Matawalle da ayyukan ‘yan bindiga, amma daga baya aka tabbatar da cewa zarge-zargen ba su da tushe
Ta kuma nuna cewa ci gaba da riƙe muƙami da yake yi a gwamnatin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, hujja ce da ke nuna gaskiyarsa da ƙwarewarsa a hidimar ƙasa.
A cewar sanarwar, hukumomin tsaro na Najeriya ƙwararru ne masu bin gaskiya, kuma da akwai wani abu a cikin zarge-zargen, da tuni an gudanar da bincike tare da ɗaukar mataki.
Sanarwar ta kuma yabawa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa damar da yake bai wa ‘yan ƙasa masu kishin ƙasa, tare da jinjina wa Ministan Tsaro, Christopher Musa, da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, bisa ƙoƙarinsu wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
A ƙarshe, an yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da mara wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu baya domin cigaban ƙasa.




