DSS Ta Ceto Sakataren Karamar Hukumar Kibiya Bayan Garkuwa dashi a Kano

Jami’an tsaro na DSS sun samu nasarar ceto Sakataren Karamar Hukumar Kibiya bayan wani samame da suka kai a yankin Rano na Jihar Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa an sace jami’in ne kwanaki kaɗan da suka gabata a gidansa da ke Kibiya, inda masu garkuwar suka bukaci kudin fansa har naira miliyan 100 domin sakin sa.
Majiyoyin tsaro sun ce ana zargin masu garkuwar sun gano inda yake ne ta hanyar bayanan cikin gida daga wani mazaunin yankin.
Haka kuma, bayanan sirri sun nuna cewa maharan sun fito ne daga yankin Rijana, wuri da aka dade ana danganta shi da ayyukan ta’addanci a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Bayan samun sahihan bayanai, jami’an DSS sun gano maboyar masu garkuwar a Rano, inda suka kai farmaki da safiyar ranar Talata.
A yayin samamen, an yi musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da maharan.
Duk da haka, jami’an tsaron sun samu nasarar ceto wanda aka sace cikin koshin lafiya, tare da kama mutum biyu daga cikin masu garkuwar, yayin da wasu biyu suka tsere bayan sun jikkata.
An tabbatar da cewa wanda aka ceto yana cikin koshin lafiya, kuma yana karɓar kulawar likitoci kafin a mayar da shi ga iyalansa.
A gefe guda, gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada aniyar ta na magance matsalar tsaro, inda ta yi alkawarin ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshen garkuwa da mutane da ayyukan ‘yan bindiga a fadin jihar.




