Labarai

Sojoji Sun Kashe Kwamandan Boko Haram Abdullahi Mafa a Borno

Dakarun Sojojin Najeriya sun kashe wani kwamandan ƙungiyar Boko Haram mai suna Abdullahi Mafa a yayin hare-haren da suke ci gaba da kai wa ‘yan ta’adda a jihohin Borno da Adamawa.

Mai magana da yawun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai, Laftanar Kanal Sani Uba, ya bayyana cewa an kashe Mafa ne a yankin kogin Visik da ke ƙaramar hukumar Madagali.

 

A cewarsa, bayan artabun, dakarun sun ƙwace bindigar AK-47 tare da alburusai daga hannunsa.

 

Sanarwar ta kuma ce sojojin sun kama wani da ake zargi mai suna Dauda Usman Gubula, wanda ake zargin yana samar wa ‘yan ta’adda jirage marasa matuƙa da ake gyarawa domin kai hare-hare.

An ce an same shi da jirage marasa matuƙa guda biyu tare da kayan haɗinsu, da kuma na’urar samar da wutar lantarki ta hasken rana guda 20.

Rundunar ta tabbatar da cewa hare-haren na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na murƙushe ragowar ‘yan ta’adda da dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button