Labarai

Rahoto: Sojoji Sun Karyata Labarin Harin Gidan Bishop Kukah a Sokoto

Rundunar Sojin Najeriya ta 8 Division tare da Sector 2 na Operation FANSAN YAMMA sun karyata wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ya yi zargin cewa an kai hari gidan Matthew Kukah da kuma Cocin Katolika na Sokoto.

A cikin wata sanarwa da mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar, Olaniyi Osoba ya fitar, ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya mara tushe, yana mai cewa babu wani hari da ya faru a Jihar Sokoto.

Sanarwar ta tabbatar da cewa Bishop Kukah na cikin koshin lafiya, kuma yana gudanar da ayyukan bukukuwan Easter ba tare da wata matsala ba.

Rundunar ta kuma jaddada cewa tana aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya ga al’ummar jihar, tare da tabbatar da cewa an ɗauki matakan tsaro masu ƙarfi domin ganin an gudanar da bukukuwan Easter cikin lumana.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button