Labarai

Rikicin Masarautar Kano: Hakikanin abun da ya faru a zaman kotun Koli

Kotun Koli ta Najeriya ta dage sauraron shari’ar masarautar Kano zuwa ranar 17 ga Afrilu, 2027.

 

Rahotanni sun ce Mai shari’a Adamu Jauro, wanda ke jagorantar sauraron karar, ne ya sanar da dage shari’ar domin ci gaba da sauraro a sabuwar ranar da aka sanya.

 

An tsara sauraron karar ne da farko a yau Litinin, sai dai ba a samu damar ci gaba da shari’ar ba, bayan da lauyan daya daga cikin wadanda ake kara ya shigar da wata bukata a ranar 14 ga Afrilu, sannan ya mika wa lauyan masu kara takardun a ranar 15 ga Afrilu, 2026.

 

Bisa dokokin kotu, bangaren da aka mika wa wannan bukata na da kwanaki 14 domin mayar da martani, lamarin da ya sa aka dage zaman.

 

Da yake zantawa da SolaceBase, lauyan masu kara, Barista Mamman Lawan Yusufari, ya ce an zauna shari’ar ne don sauraro, ba don yanke hukunci ba kamar yadda mutane da dama suka dauka.

 

Ya ce: “An zauna ne yau don a saurari karar ba wai yanke hukunci ba. Lauyan daya daga cikin wadanda ake kara ya shigar da wata bukata a ranar 14 ga Afrilu, sannan ya ba mu kwafin takardun washegari. Doka ta ba mu damar mayar da martani cikin kwanaki 14, shi ya sa aka dage sauraron.”

 

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito A watan Mayun 2024 ne gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sake nada Malam Muhammadu Sanusi na II a matsayin Sarkin Kano na 16, bayan rushe dokar da ta kawo Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda shi ne Sarkin Kano na 15.

 

Tun da farko dai gwamnatin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta tube Muhammadu Sanusi na II daga sarauta a ranar 9 ga Maris, 2020.

 

Haka kuma gwamnan ya yi wa dokar masarautar Kano gyara.

 

Bayan hakan ne aka fara shari’o’i domin kalubalantar tube Aminu Ado Bayero daga sarauta.

 

A hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke kan lamarin, ta ce Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ba ta da hurumin tsoma baki a wannan batu.

 

Hukuncin ya yiwa gwamnatin jihar Kano dadi sosai.

 

A lokacin, Babban Lauyan jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Barista Haruna Dederi, ya ce: “Wannan hukunci ya tabbatar da halaccin matakan da gwamnati ta dauka tare da fayyace hurumin kotuna kan harkokin sarauta.”

 

Shi kuwa Dan’Agundi ya shaida wa manema labarai cewa ya umarci tawagar lauyoyinsa da su daukaka kara zuwa Kotun Koli.

 

Ya ce bangaren gwamnati ya yi kuskure wajen fassara hukuncin, kasancewar gwamnati na goyon bayan Muhammadu Sanusi na II ya ci gaba da zama kan karagar mulki.

 

Haka kuma ya ce bai dace Kotun Daukaka Kara ta dauki karar a matsayin ta sarauta ba, maimakon duba ta a matsayin ta tauye hakkin dan Adam da aka shigar da ita tun asali.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button