ICPC Ta Shirya Gurfanar da Tsohon Gwamnan Kaduna El-Rufai a Kotu

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta bayyana shirinta na gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna a ranar 24 ga Maris, 2026.
A cewar hukumar, za a gurfanar da El-Rufai tare da wani mai suna Joel Adoga kan zarge-zargen da suka hada da karkatar da kadarorin gwamnati, mallakar kadarori ba bisa ka’ida ba, da kuma halasta kudaden haram.
Bugu da kari, akwai wata kara ta daban a Babbar Kotun Jihar Kaduna da ta hada shi da wani Amadu Sule, inda ake zarginsu da amfani da mukami ba daidai ba, damfara da kuma bai wa wasu gata ba bisa ka’ida ba.
ICPC ta bayyana cewa an shigar da karar ne tun a ranar 18 ga Maris, 2026, kuma an riga an mika wa El-Rufai sammaci domin ya gurfana a gaban kotu.
Hukumar ta jaddada kudirinta na yaki da cin hanci da rashawa tare da tabbatar da gaskiya da adalci a kasar.




