Labarai

Shin Da Gaske Gwamnatin Tinubu Za Ta Fara Karbar Harajin Solar?

A yayin da jita-jita ke yawo a kafafen sada zumunta cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na shirin fara karɓar haraji kan masu amfani da solar, bincike ya nuna cewa wannan batu ba gaskiya ba ne.

A halin yanzu, babu wata doka a hukumance da ta tilasta wa ‘yan Najeriya biyan wani haraji na musamman saboda amfani da solar a gidajensu.

Haka kuma, ba a buƙatar izini daga gwamnati kafin mutum ya sayi ko ya girka solar domin amfanin gida.

Rahotanni sun nuna cewa asalin wannan jita-jita ya samo ne daga wasu tsare-tsare da dokokin Nigerian Electricity Regulatory Commission (NERC), waɗanda suka shafi manyan kamfanoni da masana’antu masu amfani da manyan tsarin solar masu ƙarfi, musamman waɗanda suka haura MegaWatt 1.

 

 

Haka kuma, dokokin sun shafi tsarin haɗa solar da lantarkin gwamnati (net metering), inda masu irin wannan tsarin ke buƙatar yin rajista tare da bin ƙa’idoji na musamman.

 

 

Bugu da ƙari, akwai batun karin kuɗin harajin shigo da kayan solar daga ƙasashen waje, wanda ya haɗa da wasu sabbin tsare-tsaren haraji domin kare masana’antun cikin gida.

 

Sai dai wannan ya shafi masu shigo da kaya ne, ba masu amfani da solar a gidajensu ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button