Siyasa
Tinubu ya umarci masu son takara a 2027 da su ajiye mukamansu

Shugaban ƙasar Nigeria, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya umarci dukkanin masu riƙe da muƙaman siyasa a ƙarƙashin gwamnatinsa da ke da niyyar tsayawa takara a zaɓukan shekarar 2027 da su ajiye mukamansu kafin ranar 31 ga watan Maris.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Dewan Goshit, shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF), ya fitar a ranar Talata.
Jaridar The Cable ta rawaito cewa, sanarwar ta ce matakin na da nufin tabbatar da gaskiya, daidaito da kuma bai wa duk masu neman takara damar fafatawa cikin yanayi mai adalci kafin fara shirye-shiryen zaɓe.




