Labarai
Gwamnatin Kano Ta Ware Naira Miliyan 99 Don Yi Wa Karnuka Rigakafi

Kwamishinan Ma’aikatar Kiwon Dabbobi ta Jihar Kano, Aliyu Isa Aliyu, ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta fara aiwatar da shirin yi wa karnuka dubu 10 rigakafin cutar rabies a matakin farko.
Ya ce an ware kimanin naira miliyan 99 da dubu hamsin da takwas domin gudanar da shirin, wanda zai haɗa da rigakafin karnukan da kuma ƙidaya yawan karnukan da ake da su a faɗin jihar.
Kwamishinan ya jaddada cewa cutar rabies, wadda mahaukacin kare ke iya yaɗawa ga ɗan Adam idan ya cije shi, na da matuƙar haɗari domin tana iya yin kisa kai tsaye idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba.
Ya ƙara da cewa wannan shiri na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na kare lafiyar al’umma tare da rage yawaitar cutar a Kano.




