Kotu Ta Tsare Direban Matar Sarki Sanusi II Kan Zargin Satar Gwala-Gwalai na Naira Miliyan 60

Kotun Majistare da ke Nomansland a ƙaramar hukumar Fagge, Jihar Kano, ta tsare wani direban matar Sarkin Kano na biyu, Muhammadu Sanusi II, tare da wasu mutum biyu bisa zargin satar gwala-gwalai da kuɗaɗe da darajarsu ta kai Naira miliyan 60.
Wadanda ake tuhumar sun haɗa da Sulaiman Yakubu Kulkude, Idris Musa da kuma Abdullahi Usaini, inda ake zarginsu da aikata laifin haɗin baki da sata.
A cewar tuhumar da aka karanta a gaban kotu, an zargi Sulaiman da shiga ɗakin matar Sarkin ba tare da izini ba, inda ya kwashe gwala-gwalai, kuɗi da kuma waya.
Rahotanni sun nuna cewa Sulaiman ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi bayan an karanta masa ƙorafin, yayin da sauran biyun suka musanta zargin.
Lauyan da ke kare wadanda ake tuhumar ya roƙi kotu da ta ba su beli, amma Mai Shari’a Halilu Abdurahman ya bayar da belin ne da wasu sharuɗa masu tsauri.
Daga cikin sharuɗan belin akwai biyan Naira miliyan 10 da kuma samar da wanda zai tsaya musu.
Kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Afrilu, tare da umartar cewa za a ci gaba da tsare su har sai sun cika sharudan belin.




