Labarai

‘yan Vigilante 6,700 ne Suke Sintiri a Kano domin tabbatar da tsaro alokutan azumi

Rundunar ’yan sintiri (Vigilante) a Jihar Kano ta bayyana cewa ta baza jami’anta sama da 6,700 a sassa daban-daban na birnin Kano da kewaye domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a lokacin azumin watan Ramadan.

Babban Kwamandan rundunar a jihar, Shehu Rabiu, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai, inda ya ce an ɗauki matakin ne domin ƙarfafa tsaro musamman a lokutan ibada.

A cewarsa, wasu daga cikin jami’an na sanye da kayan sarki, yayin da wasu ke aiki cikin fararen kaya, musamman a wuraren gudanar da Sallar Asham da kuma sintiri a cikin unguwanni.

 

Ya kuma yi kira ga iyaye da su ja kunnen ‘ya’yansu, musamman masu buga wasan wuta (knockout) da masu kaɗa kiɗan gwauro a lokacin ibadar Sallar Asham, domin kaucewa tayar da hankalin jama’a da haddasa tashin hankali.

Rundunar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin ganin an gudanar da watan Ramadan cikin lumana da kwanciyar hankali a faɗin jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button