Labarai

Majalisar Karamar Hukumar Bagwai Ta Rufe Kasuwar Dan Dabino Saboda Dalilan Tsaro

Majalisar Karamar Hukumar Bagwai a Jihar Kano ta sanar da rufe Kasuwar Dan Dabino da ke Mazabar Kiyawa na wucin gadi bisa dalilan tsaro.

Rahoton da Arewa Updates ta rawaito ya bayyana cewa sanarwar na kunshe ne a cikin wata takarda da Jami’in Yada Labarai na karamar hukumar, Shehu Bello Shanono, ya fitar a ranar Asabar 14 ga Fabrairu, 2026.

Sanarwar ta ce Jami’in Tattara Kudin Shiga na karamar hukumar, Malam Abubakar Auwal R.O., shi ne ya sanar da daukar matakin, bayan samun sahihan bayanan tsaro da ke nuni da yiwuwar barazana a wata karamar hukuma mai makotaka da Bagwai.

A cewarsa, matakin rufe kasuwar an dauke shi ne domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasuwa da mazauna yankin, tare da bai wa jami’an tsaro damar gudanar da bincike da daukar matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya.

Majalisar ta kara da cewa kasuwar za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai jami’an tsaro sun tabbatar da cewa an dawo da cikakken tsaro da kwanciyar hankali a yankin.

Haka kuma, ta bukaci mazauna yankin da ‘yan kasuwa su bai wa jami’an tsaro cikakken hadin kai tare da bin doka da oda domin tabbatar da tsaro mai dorewa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button