Matsayar Trump game da Iran ta bayyana rarrabuwar kawuna
Matsayar ƙasar Amurka na ganin kamata ta shiga tare da taimakawa Isra’ila wajen kai hari kan Iran, ko kuma ta nisanci wannan farmaki gaba ɗaya, ta kawo rabuwar kawuna a tsakanin magoya bayan Shugaban Amurka Donald Trump.
Rahotanni sun ce shugaban na Republican yana tunanin taimakawa wajen kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, bayan wata ganawa da ya yi da masu ba shi shawara kan harkokin tsaro a fadar White House ranar Talata.
Yiwuwar cewa zai iya jawo Amurka cikin wani rikicin kasashen waje ya sanya bangaren ba ruwanmu da masu tsaurin ra’ayi a jam’iyyarsa cikin tsananin rikici da juna.
A ranar Talata, dan majalisar wakilai na jam’iyyar Republican mai ra’ayin mazan jiya, Thomas Massie daga Kentucky, ya hade kai da ‘yan jam’iyyar Democrat don gabatar da kudirin doka da zai hana Trump shiga cikin “rikicin da ba a amince da shi ba” da Iran ba tare da amincewar majalisar dokoki ba.
“Wannan ba yaƙinmu bane. Ko da ace haka ne, dole ne Majalisar Dokoki ta yanke hukunci kan al’amuran bisa tanadin Kundin Tsarin Mulkinmu,” Massie ya wallafa a kan X.




