Labarai

Tallafin Gwamnati Na Musamman Ya Bankado Gibin Tsarin Lafiya’a jihar Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta dauki nauyin kula da lafiyar wata mata mai jego, Hafsatu Yusuf, wadda ta haifi yara biyar a Murtala Specialist Hospital.

 

Mijin ta, Salisu Nufi’u, ya bayyana jin dadinsa da matakin da gwamnati ta dauka, yana mai cewa taimakon ya zo a lokacin da suka fi bukata.

 

Rahotanni sun tabbatar da cewa uwa da jariran na samun kulawa ta musamman daga likitoci domin tabbatar da lafiyarsu.

 

Sai dai, duk da wannan dauki da gwamnati ta yi, al’umma na ci gaba da nuna damuwa kan yadda ake samun irin wadannan labarai ne kawai a lokutan da suka zama na musamman, lamarin da ke bayyana gibin da ke akwai a tsarin kula da lafiya, musamman ga talakawa.

 

Masu sharhi na ganin cewa yawan matsalolin da mata masu juna biyu ke fuskanta a asibitoci, da kuma karancin kayan aiki da ma’aikata, na nuna cewa har yanzu akwai bukatar kara zuba jari mai yawa a bangaren lafiya.

 

Wannan lamari ya sake jawo kira ga gwamnatin jihar da ta mayar da hankali wajen samar da ingantaccen tsarin lafiya mai dorewa, ba tare da jiran irin wadannan lokuta na musamman ba.

 

Duk da haka, gwamnatin ta jaddada kudurinta na ci gaba da tallafawa al’umma, musamman masu karamin karfi, domin tabbatar da samun ingantaccen kiwon lafiya a fadin jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button