Labarai

APC Ta jefa ‘yan Nigeria cikin kuncin da basu taba ganiba, cewar Rotimi Amaechi.

Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa halin rayuwa a Najeriya ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙazanta matuƙa, har ta kai ga mutane na nuna sha’awar komowar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, kan mulki.

A yayin wata hira da manema labarai a birnin Abuja, Amaechi ya ce lamarin tattalin arzikin ƙasar ya tabarbare, inda hauhawar farashin kayayyaki da ƙarancin kuɗi suka jefa miliyoyin ‘yan ƙasa cikin ƙunci da yunwa.

Farashin abinci da sauran kayayyaki ya tashi fiye da kima, mutane ba za su iya siyan kayan da suke buƙata. Komai ya rushe,” in ji Amaechi.

Ya ƙara da cewa wahalhalun da ake ciki sun sa jama’a na bukatar dawowar mulkin Buhari.

Yanzu mutane na muradin Buhari ya dawo. A kullum, gwamnatin da ke zuwa tana yi wa mutane muni fiye da wadda ta gabata. Wannan ne yasa mutane ke ci gaba da tunanin gwamnatin baya,” in ji shi.

Amaechi ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar APC a daren Talata, inda ya sanar da komawarsa jam’iyyar haɗaka ta ADC.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button