Ketare

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon ruwan sama a Koriya ta Kudu ya karu zuwa 18 yayin da hukumar yanayi ta gargadi game da zazzafar rana

Ruwan sama mai tsanani da ya sauka a Koriya ta Kudu ya kashe akalla mutane 18 sannan wasu tara ba a san inda suke ba, in ji hukumomi, yayin da gwamnati ta dage da gargadin samun ruwan sama mai yawa kuma hukumar yanayi ta yi gargadin dawowar zafin rana a kudancin kasar.

Ana cigaba a aikin Ceto ya zuwa ranar Litinin yayin da sojojin Koriya ta Kudu suka sanar da tura dubban sojoji zuwa wuraren da ruwan sama ya lalata don taimakawa a kokarin farfadowa da yankunan.

Ruwan sama mai karfi ya fara a ranar 16 ga Yuli kuma ya kawo wasu daga cikin mafi tsananin ruwan sama na sa’a guda da aka taba gani a wasu daga cikin lardunan tsakiya da kudancin Koriya ta Kudu. Ruwan sama mai tsanani na tsawon kwanaki biyar ya haifar da rushe gidaje, tare da gangarowar kasa, kuma ya jawo ambaliyar ruwa mai girma ta haifar da awun gaba da motoci.

Akalla mutane 10 sun mutu a lardin kudancin Sancheong, kuma wasu mutane hudu har yanzu ba a gansu ba a can, a cewar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da Tsaro.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button