Labarai
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Abuja Ya Umarci ayi Gwajin Kwakwalwa ga Jami’ai dake aikin a Birnin

Kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya Abuja, Ahmed Sanusi, ya bayar da umarnin gudanar da gwajin lafiyar kwakwalwa ga dukkan jami’an rundunar da ke aiki a yankin.
Wannan mataki na daga cikin kokarin rundunar na kara inganta ladabtarwa, kwarewa da kuma ingancin aiki a tsakanin jami’anta, domin tabbatar da kyakkyawan gudanar da ayyukan tsaro.
Sanarwar ta fito ne ta bakin jami’ar hulda da jama’a ta rundunar, Josephine Adeh, a ranar Alhamis, inda ta bayyana cewa an dauki wannan mataki ne bayan wani taron gaggawa da ya hada kwamishinoni, kwamandojin yankuna, jami’an yanki da kuma shugabannin rundunonin dabaru.




