Kotun Tarayya Ta Daure Matashi Shekaru 8 Kan Safarar Wiwi a Kano

A cewar sanarwar da jami’in hulda da jama’a na NDLEA, Sadiq Muhammad Maigatari, ya fitar, an kama Kabir Adamu ne a ranar 14 ga Janairu, 2026, bayan jami’an Gidajen Gyaran Hali suka gano wiwi da aka ɓoye cikin biredi domin kaiwa wani da ake kira “Wizzy” wanda ke fuskantar shari’a a kotun jihar Kano da ke Miller Road.
Nan take aka mika wanda ake zargin ga NDLEA domin ci gaba da bincike da gurfanar da shi a gaban kotu.
Bayan kammala shari’a, Mai shari’a SM Shuaibu na Babbar Kotun Tarayya ya same shi da laifi, inda a ranar 22 ga Afrilu, 2026 ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru takwas ba tare da zabin tara ba.
Kwamandan NDLEA na Kano, CN DY Lawal, ya bayyana cewa hukuncin ya nuna haɗin kan hukumomin tsaro da bangaren shari’a wajen yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa zai zama darasi ga masu yunkurin aikata irin wannan laifi.
Hukumar ta kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar kai rahoton duk wani abu da ya shafi miyagun ƙwayoyi.



