Gwarzo Ya Ayyana Neman Kujerar Sanatan Kano Ta Arewa a 2027

Tsohon karamin ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Tijjani Gwarzo, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Sanatan Kano ta Arewa a zaben shekarar 2027.
Gwarzo ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 18 ga Afrilu, 2027, inda ya ce ya dauki wannan mataki ne bayan tuntuba da nazari mai zurfi tare da yin addu’a domin neman shiriya.
A halin yanzu, kujerar Sanatan Kano ta Arewa na hannun mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, wanda ke wakiltar yankin.
Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin mukarraban gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, sun halarci bikin ayyana takarar Gwarzo.
Daga cikinsu akwai Alhaji Nagoda da Murtala Zawai, da sauran masu ruwa da tsaki.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwarzo ya tabbatar da cewa zai nemi takarar ne a karkashin jam’iyyar APC, yana mai bayyana kudurinsa na kawo ci gaba da wakilci mai inganci ga al’ummar Kano ta Arewa.




