Labarai

Kotu ta umarci a saki Sheikh Sani Khalifa Zaria tare da ba shi diyyar Naira Miliyan 5

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci a saki malamin addini, Sheikh Sani Abdulkadir Zaria, ba tare da wani sharadi ba, tare da ba shi diyyar naira miliyan 5 kan take hakkin ɗan Adam da aka yi masa.

 

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a hukuncin da mai shari’a Peter O. Lifu ya yanke, kotun ta ce tsare malamin na dogon lokaci ba tare da sahihin umarnin kotu ba ya saɓa wa haƙƙoƙinsa na ‘yanci da mutunci kamar yadda kundin tsarin mulki na 1999 ya tanada.

 

Malamin ya shigar da ƙara ne kan hukumomi da suka haɗa da EFCC, DIA, da SSS tare da bankin Jaiz , bisa zargin tsare shi da kuma kulle asusunsa ba bisa ka’ida ba.

 

Kotun ta kuma umarci a biya shi naira miliyan 1 daga EFCC da Jaiz Bank kowanne, yayin da DIA da SSS za su biya naira miliyan 4 tare, baya ga umarnin su bayar da hakuri a rubuce.

 

Haka kuma an umarci Jaiz Bank da ya cire takunkumin da aka sanya wa asusun malamin nan take.

 

Lamarin ya samo asali ne daga tsare malamin tun ƙarshen 2025 bayan ya je Abuja domin warware matsalar kulle asusunsa da ake zargin yana da alaƙa da binciken wani shirin juyin mulki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button