APC Ta Ba NNPP Wa’adin Sa’o’i 72 data Janye Zargin da take mata Ko ko suhadu’kotu

Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta yi watsi da zargin da ɓangaren Kwankwasiyya na jam’iyyar NNPP ke yi na cewa gwamnatin jihar na shisshigi a harkokin shari’a, tana mai bayyana zargin a matsayin ƙarya da ɓatanci.
A wata sanarwa da kakakin APC na jihar, Auwalu Soja Gwale, ya fitar, ya ce zargin da aka ce kakakin wani ɓangare na NNPP, Ibrahim Karaye, ya yi ba shi da hujja, kuma an yi shi ne domin bata sunan ɓangaren shari’a.
Jam’iyyar APC ta musanta zargin cewa gwamnatin Kano ta bayar da kuɗaɗe masu yawa domin yin tasiri a shari’ar da ake yi a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, tare da buƙatar a janye kalaman cikin gaggawa.
Sanarwar ta kuma bai wa Karaye da NNPP wa’adin sa’o’i 72 su janye zargin, su ba da haƙuri a bainar jama’a, tare da daina irin waɗannan kalamai, tana mai gargadin cewa rashin yin hakan zai jawo shigar da ƙara kan ɓatanci.
APC ta bayyana zargin a matsayin “ƙarya, mai cike da mugunta kuma mara tushe a doka,” tana mai jaddada cewa gwamnatin Kano ba ta taɓa tsoma baki a harkokin shari’a ba.
Haka kuma, jam’iyyar ta zargi wasu daga cikin ‘yan NNPP da yin kalamai marasa tushe duk lokacin da al’amuran siyasa ba su tafi yadda suke so ba.
A ƙarshe, APC ta buƙaci ɓangaren Kwankwasiyya na NNPP da su mayar da hankali kan warware rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyar, maimakon zargin ɓangaren shari’a ba tare da hujja ba, tare da kira ga al’umma da su yi watsi da zargin.
Spotlight




