Gwamnatin Kano Ta Amince da Biyan Albashin watan Maris Da Wuri Domin Shirin Sallah

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da fara biyan albashin watan Maris na shekarar 2026 ga ma’aikatan gwamnati tun da wuri domin ba su damar shirya bukukuwan Eid al-Fitr cikin sauƙi.
A cewar Mukaddashiyar Shugabar Ma’aikatan Jihar, Bilkisu Shehu Maimota, gwamnan jihar ya bayar da umarnin sakin kuɗaɗen domin a biya dukkan ma’aikatan gwamnati ba tare da ɓata lokaci ba.
Ta bayyana cewa matakin na da nufin bai wa ma’aikata damar shirya bukukuwan Sallah cikin walwala da mutunci, tare da sauƙaƙa musu gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
Haka kuma ta ce biyan albashin da wuri na nuna yadda gwamnatin jihar ke bai wa jin daɗin ma’aikata muhimmanci tare da yaba gudunmawar da suke bayarwa wajen cigaban jihar.
Bilkisu Shehu Maimota ta kuma buƙaci ma’aikatan gwamnati da su yi amfani da wannan damar cikin hikima, tare da ƙara ƙaimi da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu domin inganta ayyukan gwamnati a jihar.
Gwamnatin ta kuma jaddada aniyarta na ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su inganta walwalar ma’aikata tare da ƙara inganta aiki a cikin harkokin gwamnati




