Dakarun sojin Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda 11 tare da lalata sansanoninsu a Borno

Rundunar Operation HADIN KAI (OPHK) ta sanar da cewa ta kashe wasu ‘yan ta’adda tare da lalata sansanoninsu a Jihar Borno, yayin da take ci gaba da kai hare-hare masu tsauri a yankin.
Jami’in yada labarai na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Maiduguri.
A cewarsa, hare-haren da aka gudanar karkashin Operation Desert Sanity V sun hada da farmakin kasa da sama a wurare daban-daban, musamman a gadar Azir da dazukan Bulabulin, tare da goyon bayan rundunar sojin sama.
Uba ya ce sojojin sun yi arangama da ‘yan ta’adda a kauyen Malam Shiri, inda suka yi amfani da dabarar kewaye su ta bangarori, lamarin da ya kai ga kashe ‘yan tada kayar baya 11, yayin da wasu da dama suka tsere da raunuka.
Ya kara da cewa farmakin ya dakile hanyoyin samar da kayayyaki da kuma rage karfin ‘yan ta’addan wajen gudanar da ayyukansu a yankin.
Hakazalika, ya ce sojojin sun sake fafatawa da ‘yan ta’adda a kan hanyar Timbuktu, a yankin Wajiroko zuwa Sabon Gari, inda suka samu galaba a dukkan arangamar da aka yi.
Daga cikin kayayyakin da aka kwato akwai bindigogin AK-47, makaman roka, alburusai masu yawa, kayan rataya harsasai da kuma na’urorin sadarwa.
Uba ya jaddada muhimmiyar rawar da rundunar sojin sama ta taka wajen samar da bayanan leken asiri da sa ido, wanda ya taimaka wajen kai hare-hare cikin tsari da kuma jagorantar ayyuka yadda ya kamata.
Ya kara da cewa a halin yanzu, sojoji tare da hadin gwiwar ‘yan sa-kai na ci gaba da farautar ‘yan ta’addan da suka tsere a yankunan Forfor, Multe da Wajiroko domin hana su sake haduwa.




