Siyasa

Rikicin Siyasa ‘a karamar hukumar Tudun Wada yayi Ajalin wani jami’in tsaro

Rikicin siyasa ya ɓarke tsakanin Hon. Alhassan Ado Doguwa da Shugabar Ƙaramar Hukumar Tudun Wada biyo bayan wani hargitsi da ya faru yayin rabon kayan abinci da Doguwa ya gudanar a yankin.

 

Rahotanni sun bayyana cewa an samu rudani a lokacin rabon kayan tallafin, lamarin da ya janyo cece-kuce tsakanin ɓangarorin biyu kan yadda aka gudanar da shirin.

 

Bayan faruwar lamarin, an kuma samu rahoton mutuwar wani jami’in Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC), wanda hakan ya ƙara tayar da kura tare da jefa batun cikin zarge-zargen siyasa.

 

Wasu ɓangarori na siyasa na zargin juna kan abin da ya haddasa hargitsin da kuma mutuwar jami’in, lamarin da ya sa al’amarin ya ɗauki sabon salo na rikicin siyasa a yankin.

 

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu cikakken bayani daga hukumomin tsaro ko kuma bangarorin da abin ya shafa kan musabbabin faruwar lamarin ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button