Muhammad Musa Inya Ya Yi Murabus Daga Manajan Daraktan Hikima Radio

Gogaggen ɗan jarida, Muhammad Musa Inya, ya yi murabus daga mukaminsa na Manajan Darakta a Hikima Radio 93.7FM da ke Kano, bayan kusan watanni biyar da hawansa kan kujerar.
Rahotanni sun nuna cewa tashar ta sanar da naɗin Inya ne a watan Satumban 2025, inda ya fara aiki a ranar 6 ga Oktoba 2025 bayan amincewar kwamitin amintattun tashar.
A lokacin naɗinsa, kwamitin ya bayyana cewa ya zaɓi Inya ne saboda gogewarsa a fannin yaɗa labarai da gudanar da shirye-shiryen rediyo, tare da hulɗa da al’umma a kafafen sadarwa.
Kwamitin ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa zai bayar da jagoranci mai tasiri wanda zai ƙara ɗaga matsayin tashar a matsayin ɗaya daga cikin manyan gidajen rediyo a Arewacin Najeriya.
Sai dai Inya ya shafe watanni biyar da kwanaki huɗu kacal a kan mukamin kafin ya ajiye aiki a ranar Talata, 10 ga Maris, 2026.
Murabus ɗinsa na zuwa ne jim kaɗan bayan wasu manyan jami’an tashar sun ajiye aikinsu, ciki har da shugaban tashar Abubakar Isah Dandago, shugaban sashen siyasa Aliyu Sufyan Alhassan da kuma shugaban sashen wasanni Isma’ila Abba Tangalashi.




