Kano: Masu Neman Kujerar Mataimakin Gwamna Sun Fara Motsi Bayan Yunkurin Tsige Aminu Abdussalam

Biyo bayan matakan da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta fara dauka na tsige Mataimakin Gwamnan Jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, tuni kura ta riga ta tashi a fagen siyasar jihar yayin da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa suka fara zawarcin wannan kujerar
Rahotanni daga majiyoyi daban-daban sun bayyana cewa tun bayan fara wannan yunkuri na majalisa, wasu fitattun ‘yan siyasa da magoya bayansu suka fara nuna sha’awa da kuma hasashen mutanen da suke ganin sun dace su maye gurbin kujerar idan har batun tsige mataimakin gwamnan ya tabbata.
Haka kuma, ana ganin yadda wasu daga cikin ‘yan siyasar ke gudanar da tattaunawa a boye tare da neman goyon bayan manyan jam’iyya da masu ruwa da tsaki a siyasar jihar.
Wannan yunkuri na nufin tabbatar da cewa sun samu damar hawa wannan kujera wadda ake gani a matsayin ginshiki a tafiyar da gwamnatin jihar.
Muhimmancin Kujerar Mataimakin Gwamna
Masana harkokin siyasa sun bayyana cewa irin wannan zawarci da ake yi yana da alaka da muhimmancin kujerar Mataimakin Gwamna.
Wannan matsayi yana taka rawa sosai wajen taimakawa gwamna wajen aiwatar da manufofin gwamnati da kuma tabbatar da daidaito a cikin tafiyar da al’amuran yau da kullum na jihar.
Jiran Tsammanin Majalisa
Duk da irin wadannan hasashe da ake yi, ana jiran yadda al’amuran za su kaya bayan kammala dukkan matakan doka da majalisar dokokin jihar ke bi dangane da batun tsige mataimakin gwamnan.
A halin yanzu, daukacin al’ummar jihar da masu ruwa da tsaki na zuba ido don ganin mataki na gaba da majalisar za ta dauka.
*Ahrasjo News




