Labarai

Kada Ku Tafi Gaban Allah Da Kiyayyar ’Yan Uwanku Musulmi — Khalifa Mukhtar Hamza Alaramma

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Mukhtar Hamza Alaramma, ya bukaci al’ummar Musulmi da su guji riƙe kiyayya a tsakaninsu, yana mai gargadin cewa bai dace Musulmi su je gaban Allah da zuciyar ƙiyayya ga ’yan uwansu Musulmi ba.

 

 

Malamin ya bayyana hakan ne yayin rufe karatun tafsirin Alƙur’ani mai girma da yake gabatarwa a duk shekara a Masallacin ’Yan Kara’e da ke garin Dawanau.

 

 

A cikin jawabinsa, Khalifa Mukhtar Hamza Alaramma ya ce bai kamata Musulmi su fifita wasu a kan ’yan uwansu Musulmi ba saboda sabanin fahimta ko rashin jituwa da ka iya tasowa a tsakaninsu.

 

 

Ya jaddada cewa lokaci ya yi da malamai za su haɗa kai waje guda domin fuskantar ƙalubalen da addinin Musulunci ke fuskanta a yau da kullum.

 

 

Malamin ya kuma yi nuni da cewa haɗin kai tsakanin malamai da al’ummar Musulmi zai taimaka wajen ƙarfafa addini da kuma kare martabarsa.

 

 

A ƙarshe, ya bukaci shugabanni da su sanya tsoron Allah a cikin shugabancinsu tare da yin adalci ga al’umma domin samun zaman lafiya da cigaba a cikin al’umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button