Siyasa

Jam’iyyar PDP zata garzaya gaban kuliya kan zargin magudi a zaban Abuja

PDP ta sanar da kafa wata ƙungiyar lauyoyi ta musamman domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a yankunan Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Matakin na zuwa ne bayan sakamakon da INEC ta bayyana, wanda ya nuna cewa ‘yan takarar APC sun lashe kujerun shugabancin ƙananan hukumomi biyar cikin shida.

Rahotanni sun nuna cewa APC ta yi nasara a ƙananan hukumomin Abaji, AMAC, Bwari, Kwali da Kuje, yayin da PDP ta samu nasara a Gwagwalada kaɗai.

An gudanar da zaɓen ne domin cike kujerun shugabanni shida da na kansiloli 62.

Jam’iyyar PDP ta ce zaɓen ya gudana cikin yanayi na ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri’a da kuma rahotannin sayen ƙuri’u.

A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Ini Ememobong, ya fitar, jam’iyyar ta taya waɗanda suka yi nasara murna, amma ta jaddada cewa akwai kura-kurai a sakamakon zaɓen.

Sanarwar ta ƙara da cewa ƙungiyar lauyoyin jam’iyyar za ta kasance ƙarƙashin jagorancin mai ba ta shawara kan harkokin shari’a na ƙasa, Shafi Bara’u, tare da kira ga duk ‘yan takarar da ke da ƙorafi su gaggauta gabatar da su domin ɗaukar mataki na shari’a.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button