Labarai

Tinubu Ya Tsige Egbetokun, Ya Naɗa Tunji Disu A Matsayin Sabon Sufeto Janar

Shugaban Ƙasar Bola Ahmed Tinubu, ya tsige Sufeto Janar na ’Yan Sandan ƙasar, Kayode Egbetokun, daga mukaminsa.

Majiyoyi daga cikin manyan jami’an tsaro da kuma Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda (Police Service Commission) sun tabbatar da cewa an umurci Egbetokun da ya fara shirye-shiryen miƙa mulki, bayan wata ganawa da ya yi da shugaban ƙasa a Fadar Shugaban Ƙasa.

Rahotanni sun ce ana sa ran tsohon shugaban rundunar zai kammala miƙa ragamar aiki cikin kankanin lokaci.

A cewar majiyoyin, an naɗa Tunji Disu a matsayin sabon Sufeto Janar na ’Yan Sanda. Kafin wannan naɗi, Disu shi ne Mataimakin Sufeto Janar mai kula da sashen binciken manyan laifuka na rundunar ’yan sanda da ke Alagbon a Jihar Legas.

Wasu rahotanni sun nuna cewa an shawarci Egbetokun da ya sauka domin ya mayar da hankali kan lafiyarsa, yayin da wasu jami’an rundunar suka bayyana goyon bayansu ga sauyin shugabancin.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a fitar da cikakkiyar sanarwa a hukumance daga Fadar Shugaban Ƙasa ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button