Labarai

Tinubu Ya Ayya­na 2026 a Matsayin Shekarar Iyali da Cigaban Al’umma

Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda ya jaddada cewa ƙarfafa ginshikin iyali na da matuƙar muhimmanci wajen samar da ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa, tsaron ƙasa da haɗin kan al’umma.

Tinubu ya umarci dukkan matakan gwamnati da su daidaita tsare-tsarensu da shirye-shiryensu da wannan sabon tsari, yana mai nuni da cewa ƙasashe da dama kamar Turkiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa da Masar sun rungumi manufofin da ke bai wa iyali muhimmanci domin samun ci gaba na dogon lokaci.

Ya ƙara da cewa matakin zai sauya fifikon manufofin jin ƙai, inda ma’aikatun gwamnati za su karkata kasafin kuɗi da shirye-shiryensu zuwa tallafa wa iyalai kai tsaye.

A nata ɓangaren, Ministar Harkokin Mata da Cigaban Zamantakewa, Hajiya Imaan Sulaiman Ibrahim, ta bayyana cewa an riga an fara aiwatar da sabon tsari, tare da shirin ƙaddamar da Nigeria Families First Programme, wanda zai mayar da hankali kan tallafin tattalin arziki, tarbiyya, kiwon lafiya, gidaje da kariyar zamantakewa, a matsayin wani muhimmin ɓangare na ajandar Renewed Hope ta gwamnatin Tinubu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button