KEDCO Ta Sanar da cewa za’a sami Karancin Wutar Lantarki a Kano, Katsina da Jigawa

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano, Kano Electricity Distribution Company (KEDCO), ya sanar da cewa za a fuskanci ƙarancin wutar lantarki a jihohin Kano
Katsina da Jigawa
A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar 22 ga Afrilu, 2026, ya bayyana cewa matsalar ta samo asali ne daga raguwar wutar lantarki da ake samu daga cibiyar lantarki ta ƙasa, lamarin da ya shafi rabon wuta a yankunan da yake kula da su.
Kamfanin ya ce adadin wutar da ake bai wa kamfanin ya ragu zuwa kusan megawatt 200, wanda hakan ya sa ba zai iya biyan bukatar kwastomomi gaba ɗaya ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa an fara amfani da tsarin rarraba wuta gwargwadon yadda ake samu, wanda hakan zai iya janyo katsewar wuta lokaci zuwa lokaci.
Kamfanin ya bayyana cewa yana ci gaba da tattaunawa da hukumomin da ke kula da samar da lantarki domin samun ƙarin wuta, tare da tabbatar da cewa za a dawo da wadatacciyar wuta da zarar an gyara matsalolin da ke bangaren samar da lantarki.
KEDCO ya kuma buƙaci al’umma da su yi haƙuri da halin da ake ciki yayin da ake kokarin shawo kan matsalar.



