’Yan Sanda Sun NemI Haɗin Kan Al’umma Don Murkushe Fadan Daba a Kano

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta gudanar da wani taron manyan masu ruwa da tsaki domin lalubo hanyoyin magance matsalar fadan daba da ke addabar wasu unguwanni a cikin birnin Kano, musamman a yankunan Dala, Jakara da Mandawari.
Taron, wanda ya zo bisa umarnin Sufeto Janar na ’Yan Sanda kan tsarin aikin ’yan sanda na haɗin gwiwa da al’umma, ya samu halartar hakimai, shugabannin al’umma da kuma wakilan ƙungiyoyin matasa.
A yayin taron, an tattauna manyan ƙalubalen tsaro da ke haddasa rikice-rikicen daba, tare da gabatar da shawarwari masu amfani domin shawo kan lamarin.
Daga cikin shawarwarin da aka cimma akwai buƙatar iyaye da masu riƙon yara su ɗauki alhakin tarbiyyar ’ya’yansu, da kuma haɗin gwiwa wajen gano tare da cafke shugabannin ƙungiyoyin daba da ke haddasa tashin hankali.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, wanda Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda mai kula da Ayyuka, DCP Lawal Isah Mani, ya wakilta, ya jaddada ƙudirin rundunar na kawo ƙarshen laifukan daba a jihar.
Ya kuma sanar da kafa wani kwamiti da zai duba shawarwarin da aka bayar tare da aiwatar da su cikin haɗin gwiwa da shugabannin al’umma.
Taron ya ƙare da alƙawarin haɗa kai tsakanin ’yan sanda da al’umma domin dakile ayyukan fadan daba da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankunan da abin ya shafa.




