Siyasa
APCn Kano Ta Kaddamar da Kwamitin Rijistar Mambobi Na E-Register Mai Mutum 14

Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano, ta kaddamar da wani kwamiti mai mutum 14 da zai kula da aikin Rijistar Mambobi ta a faɗin jihar.
Shugaban jam’iyyar na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ne ya jagoranci kaddamar da kwamitin, inda ya bayyana cewa an kafa shi ne domin tabbatar da nasarar aikin rijistar mambobin jam’iyyar. Ya kuma yi kira ga mambobin kwamitin da su yi aiki tukuru don ganin an cimma wannan buri.
**Jagororin Kwamitin da Mambobinsa**
Kwamitin, wanda Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi ke jagoranta a matsayin Shugaba, an ce zai gudanar da aikin ne a dukkanin mazabu da ke cikin Kananan Hukumomi 44 na Jihar Kano.



