Gwamna Abba ya magantu kan zargin rabon tallafin “dan kamfai” ga mata a lokacin ziyarar Remi Tinubu

Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, ya nesanta kansa daga zargin cewa gwamnatinsa ta raba wa mata Dan kamfai ja a matsayin tallafi, yana mai cewa abin da ya faru, ya faru ne ba tare da saninsa ko amincewarsa ba.
Rahoton DAILY NIGERIAN ya bayyana cewa an ga wasu matasa mata suna daga Dan kamfai ja yayin wani gangami da aka shirya domin karrama Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu.
Ko da yake gwamnan ya musanta cewa da saninsa kan lamarin, an gan shi yana gabatar da wata mai jagorantar daga Dan kamfen, Teema Cool, ga Uwargidan Shugaban Ƙasa.
Hotuna da bidiyoyin lamarin sun bazu cikin sauri a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka dauka a matsayin wani bangare na shirin tallafawa mata.
Sai dai majiyoyi sun bayyana cewa an nuna dan kamfen ne a matsayin izgili ga tsohon uban gidansa a siyasa, Rabiu Kwankwaso. A yayin gangamin, an rawaito cewa matan sun rika rera “Dankamfen Tsula”, kalmar da ake danganta ta da Kwankwaso.
Da yake jawabi a wani taron addu’a na musamman a gidan gwamnati na Kano, Yusuf ya ce bai da masaniya kan abin da ya faru, tare da bayyana shi a matsayin abin da ya sabawa al’ada da kuma koyarwar addinin Musulunci.
Ya ce, “Mun ji abin da ya faru. Muna cikin harkokinmu sai aka sanar da ni cewa wasu mata sun fito da wasu abubuwa… Gwamna bai sani ba. Na ma daina amfani da kafafen sada zumunta saboda irin wannan abu. Na fi son a rika kawo min irin wannan bayani kai tsaye.”
Ya kara da cewa dole ne a yi Allah wadai da lamarin domin ya sabawa al’ada da koyarwar Musulunci.
Gwamnan ya ce da ya samu labarin abin da ya faru, ya gayyaci matan domin su bayyana kansu.
Daga bisani, an ga matan suna karanta Alƙur’ani mai girma tare da yin addu’o’i da neman gafara kan abin da suka aikata.




