Kotu Ta Aike da Kwamishinan Kuɗin Bauchi Gidan Yarin Kuje

Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci a mayar da Kwamishinan Kuɗi na Jihar Bauchi, Yakubu Adamu, zuwa gidan gyaran hali na Kuje duk da ba shi beli na naira miliyan 500, sakamakon rashin cika sharuɗɗan belin.
Alkalin kotun, Justice Emeka Nwite, ya bayyana cewa za a tsare Adamu har sai ya cika sharuɗɗan belin da suka haɗa da samar da masu tsaya masa biyu masu kadarori a yankunan Maitama, Asokoro ko Gwarimpa a Abuja, tare da tantance takardun kadarorinsu.
Kotun ta kuma umarce shi da miƙa fasfofinsa ga rajistarar kotu, tare da hana shi fita daga ƙasar ba tare da izini ba.
Hukumar EFCC na tuhumar Adamu da wani kamfani da badaƙalar kuɗi sama da naira biliyan 4.6, inda ake zarginsa da taimakawa wajen karkatar da kuɗin da aka ware domin sayen babura ga gwamnatin Bauchi a 2023.



