Labarai

Wata kotu ta yankewa Samha m inuwa hukuncin daurin watanni 6 a Gidan gyaran hali

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke wa jarumar Kannywood, Sa’adatu Mohammed Inuwa (wadda aka fi sani da Samha Inuwa), hukuncin daurin watanni shida bisa laifin wulakantawa da lalata takardar kuɗin Najeriya.

 

Mai shari’a S.M. Shuaibu ne ya yanke hukuncin a ranar Juma’a, 13 ga Fabrairu, 2026, bayan samun jarumar da laifi kan tuhuma guda ɗaya da ta shafi lalata takardar Naira N1000.

 

An gurfanar da ita ne bisa zargin saɓa wa tanade-tanaden Dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta shekarar 2007, musamman sashe na 21(1), wanda ya haramta lalata kuɗin ƙasa.

 

Tuhumar ta ce a shekarar 2022, a cikin hurumin kotun, ta lalata takardar Naira dubu ɗaya ta hanyar face majina da hanci, lamarin da ya saɓa da doka.

 

Bayan an karanta mata tuhumar, Samha Inuwa ta amsa laifin.

 

Lauyan masu gabatar da ƙara, Musa Isah, ya gabatar da hujjojin shari’ar tare da roƙon kotu ta yanke hukuncin da ya dace.

A nata ɓangaren, jarumar ta roƙi kotu da ta tausaya mata, tana mai bayyana cewa wannan ne karo na farko da ta aikata laifi, tare da nuna nadama kan abin da ta yi.

 

Daga bisani, Alƙali Shuaibu ya yanke mata hukuncin daurin watanni shida, tare da zaɓin biyan tara ta Naira dubu dari biyu (N200,000) a maimakon zaman gidan yari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button