Majalisar dokokin Amurka ta fara binciken hare-haren jiragen sama da Trump ya kai Najeriya

Mambobin majalisar Dokokin Amurka sun bukaci Ma’aikatar Tsaron kasar (Pentagon) ta yi bayani dalla-dalla kan hare-haren saman da Amurka ta kai a Najeriya a ranar 25 ga Disamba, 2025, tare da karin haske kan rawar sojin Amurka a kasar.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa a baya, shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa sojojin kasarsa sun kai hare-hare kan mayakan da ke da alaka da ISIS a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya. Gwamnatin Tarayya ta Najeriya ta ce an yi aikin ne da izininta, kuma bai saba wa ikon kasar ba.
Sai dai a wata wasika da ‘yan majalisar suka aike a ranar 9 ga Maris, 2026, karkashin jagorancin Sara Jacobs da Jason Crow, sun nemi karin bayani kan tushen doka da aka yi amfani da shi wajen kai harin, hadin gwiwar da aka yi da hukumomin Najeriya, da kuma yiwuwar jikkata fararen hula.
‘Yan majalisar sun kuma nuna shakku kan ikirarin cewa hare-haren sun kai ga ‘yan ISIS, inda suka ce babu kwakkwarar hujja da ke nuna akwai karfin kungiyar a jihar Sokoto.
Rahotanni sun kuma nuna cewa wasu makamai masu linzami sun gaza kai hari yadda ya kamata, inda wasu suka fadi a gonaki da gidajen jama’a, lamarin da ya kara jawo damuwa kan yiwuwar janyo asarar rayuka.
Bugu da kari, an ce Amurka na shirin tura kusan sojoji 200 zuwa Najeriya domin horas da sojojin kasar, baya ga sauran ayyukan tattara bayanan sirri da take yi.
Majalisar ta bukaci Pentagon ta yi bayani kan adadin hare-haren da aka kai, wadanda aka kashe ko suka jikkata, kudin da aka kashe, da kuma shirin Amurka na gaba a Najeriya.
Har zuwa yanzu, ba a tabbatar da ko Pentagon ta mayar da martani ga wadannan tambayoyi ba.




