Ƴansanda sun gurfanar da shugaban tsagin PDP na ƙasa kan zargin bayar da bayanan ƙarya

‘Yansanda a Najeriya sun gurfanar da tsohon minista kuma shugaban tsagin jam’iyyar PDP, Kabir Turaki, a gaban babbar kotun Abuja kan zargin gabatar da ƙorafi mai ɗauke da bayanan ƙarya ga sufeton ‘yansanda a shekarar 2022.
Jaridar Premium Times ta rawaito cewa Turaki ya musanta zargin da ake masa, yayin da alkalin kotun, Peter Kekemeke, ya bada belinsa kan naira miliyan 100 tare da sharadin gabatar da mai tsaya masa.
Kotun ta ce lauyansa ya nuna cewa yana da ‘yancin beli, kuma bai guje wa shari’a ba duk da rashin halartar zaman da ya gabata. Sai dai lauyan masu gabatar da ƙara ya bukaci a tsare shi, amma kotu ta yi watsi da wannan bukata.
An ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 11 ga Yuni domin ci gaba da shari’a.
A gefe guda, shari’ar na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin shugabancin jam’iyyar PDP ke gaban Kotun Koli, inda Turaki ke cikin masu fafutukar neman a amince da ɓangarensu a matsayin halattaccen shugabanci.



